A jiya ne mahukuntan kasar Sin suka gabatar da wani kundi da zai taimaka wajen bullo da wasu muhimman matakai guda uku da za su kai ga inganta harkokin kirkire-kirkire a kasar.
Kundin wanda kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar suka wallafa tare, na farko ya lashi takwabin sanya kasar Sin zama kasar da ta shahara a bangaren kirkire-kirkire nan da shekarar 2020. Na biyu yana fatan ganin kasar Sin ta kasance kan gaba a sha'anin kirkire-kirkire a duniya. Na uku, kundin ya kuduri aniyar sanya kasar Sin kasancewa jagora a bangaren kimiyya da fasahar kere-kere a duniya nan da shekara 2050.
A cewar kundin, inganta sha'anin kirkire-kirkire shi ne matakin farko na samun ci gaba. Don haka, muhimmin kundin yana kira da a hade duk wani kirkire-kirkire na sha'anin kimiyya da bangarorin kere-kere da tsare-tsare gudanarwa da na kasuwanci waje guda.
Bugu da kari, kundin ya bukaci a yi kokarin bullo da sabbin dabarun samun bunkasuwa tare da bullo da sabbin tsarin kirkire-kirkire na kasa.(Ibrahim)