Har wa yau cikin ayyukan da kasar ta Sin ke gudanarwa game da binciken sararin samaniya, ana shirin harba wani kunbon mai suna Shenzhou mai lamba 11, wanda zai tashi dauke da 'yan sama jannati biyu a karshen shekarar nan, wanda shi ma zai hade da kumbon Tiangong mai lamba 2.
Majiyarmu ta bayyana cewa bayan wani gwaji da aka yi wa na'urar harba kumbuna ta Long March mai lamba 7, a cibiyar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin, za a yi amfani da wannan na'ura wajen harba kumbon dakon kaya na Tiangong mai lamba 1, a watannin farko na rabin shekarar 2017, kumbon da shi ma zai hade da Tiangong mai lamba 2, duka dai a ci gaban da kasar ke samu a fannin gudanar da binciken kimiyyar sararin samaniya. (Saminu Alhassan)