in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban bankin Zimbabwe zai shigar da takadun kudin ajiya a ranar Litinin
2016-11-27 13:07:40 cri
Babban bankin Zimbabwe ya sanar a ranar Asabar cewa takardun kudin ajiya na dala za a shigar da su a kasuwanni a ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba, domin kawo karshen hada hadar wadannan kudi ta bayan fage ta tsawon watanni.

Babban bankin ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa takardun kudin za a shigar dasu ta hanyoyin bankunan gwamnati ta hanyar kananan takardun kudi na dala 2 da dala 5.

Shigar da takardun kudin ajiya na farko zai kasance bisa wani adadi na dalar Amurka miliyan 10 na kananan takardun kudi na dala 2, kana da miliyan 20 na kwandalayen dala guda, in ji babban bankin. Bankin ya bayyana cewa matakin janyewa daya bayan daya na takardun kudin za a takaita shi a iyakar dalar Amurka 50 a kowace rana kana dalar Amurka 150 a kowane mako domin kawar da wuce gona da iri.

Takardun kudin ajiya, da za a yi cinikinsu daidai da dalar Amurka, na samun goyon baya ta hanyar rancen kudi na dala miliyan 200 daga Bankin kasuwancin Afrika.

A farko, babban bankin ya sanar da shirye shiryen shigar da takardun kudin a cikin watan Mayu bisa tsarin daukar matakan magance karancin kudade a cikin tattalin arziki.

Yawancin 'yan Zimbabwe na fargabar ganin cewa shigar da wadannan takardun kudi zai nufi dawowa ga kudin gida da aka yi watsi dasu a shekarar 2009 tun bayan hauhawar farashin kaya mafi tsanani. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China