in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya mika godiya ga kasar Sin kan gudummawar da ta bayar ga rundunar sojojin kasarsa ta fannin fasaha
2016-11-27 17:59:22 cri
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyana godiyarsa ga kasar Sin kan taimakon da ta baiwa rundunar sojojin kasarsa ta fannin fasaha, a yayin da yake halartar bikin kawo karshen wani kwas din hadin gwiwa na horar da kwamandoji da hafsoshi.

An gudanar da kwas din a karo na 29, kuma mutane 56 da suka halarci kwas na wannan karo, wadanda suka fito daga sassan soja da 'yan sanda na kasar Zimbabwe, tare kuma da sauran wasu kasashen Afirka, tare da mutum guda da ya zo daga kasar Nijeriya, lamarin da ya shaida cewa wannan shi ne karo na farko da kasar Nijeriya ta halarci wannan kwas. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China