Shugaba Xi ya ce, Ban ya cimma nasarori masu yawa wajen aiwatar da manufofin MDD, kuma ya samu matukar yabo bisa irin dunbun nasarorin da ya cimma a lokacin aikinsa.
Shugaban kasar ya jaddada cewa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da MDD ya kai wani babban matsayi, bisa irin mu'amalar dake tsakanin bangarorin biyu, ya kara da cewa kasar Sin za ta ci gaba da hada kai da sabon sakatare janar na MDD Antonio Guterres, domin ci gaba da karfafa hadin kan dake tsakanin kasar Sin da MDD.
Ban, wanda wa'adin aikinsa karo na biyu na shekaru 5 ke karewa a karshen wannan shekara, ya yaba da irin goyon bayan da kasar Sin ta ba shi a tsawon wa'adin aikinsa a matsayin babban magatakardan MDD.
Mista Ban ya ce, kasar Sin ta taka ma muhimmiyar rawa wajen ciyar da shirin nan na samar da dawwammen ci gaba na MDD, da inganta hadin gwiwa wajen samar da zaman lafiya a Sudan ta kudu, da kuma ba da taimako wajen yaki da sauyin yanayi a duniya. (Ahmad Fagam)