in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya aika sakon jaje ga shugaban kasar Turkiya
2016-12-14 21:12:15 cri
A jiya Talata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika wa takwaransa na kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan sako jaje, inda a cikin sahihanci ya janjantawa shugaba Erdogan da iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka ji raunuka a harin bam da aka kai a birnin Istanbul a ranar 10 ga watan. Mr. Xi ya jaddada cewa, kasar Si ta yi tir da kakkausar murya kan wannan harin na ta'addanci, tana kan matsayinta na yaki da duk wani nau'i na ta'addanci. Bugu da kari, shugaba Xi ya ce, kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa da kasar Turkiya da sauran kasashen duniya ta yadda za a dakile ayyukan ta'addanci a duk fadin duniya. (Sanusi Chen)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China