Yayin zantawar tasu a Talatar nan, shugaba Xi ya jinjinawa irin nasarar da Sin ta cimma a fannin binciken sararin samaniya, tare da jaddada muhimmancin kirkire-kirkire a wannan fanni.
Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren JKS, ya gana da 'yan sama jannatin Jing Haipeng da Chen Dong, tare da sauran masana da suka tallafa wajen gudanar da bincike, da gwajin kumbon Tiangong-2 tare da Shenzhou-11.
An dai harba kumbon Shenzhou-11 ne a ranar 17 ga watan Oktobar da ya gabata, bayan kwanaki biyu ya hade da dakin gwajin kimiyya na Tiangong-2, wanda a cikin sa ne Jing da Chen suka shafe kwanaki 30 suka gudanar da aikin gwaje gwaje, kwanakin da suka zamo mafiya tsayi, da wasu 'yan sama jannatin kasar Sin suka taba shafewa a tashar bincike ta sararin samaniya.