in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya aikawa takwaransa na Jamus sakon ta'aziya
2016-12-21 09:26:55 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aikawa takwaransa na kasar Jamus Joachim Gauk sakon ta'aziya, dangane da mummunan harin nan da aka kai kan wata kasuwar Kirsimati makare da jama'a da maso yawon bude ido a birnin Berlin.

A cikin sakon, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kadu matuka da samun labarin yadda wata babbar mota ta kutsa cikin kasuwar a ranar Litinin, har mutane da dama suka mutu.

Ya ce, a madadinsa, da gwamnatin kasar Sin da, daukacin al'ummar Sinawa, yana mika sakon ta'aziya ga iyalan wadanda suka mutu tare da jajantawa iyalan wadanda suka jikkata sanadiyar wannan danyen aiki.

Shugaban na kasar ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana adawa da duk wani nau'i na ta'addanci, kuma tana goyon bayan kasar Jamus a kokarin da ta ke yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kana a shirye ta ke ta karfafa hadin gwiwa da sauran kasashen duniya, ciki har da kasar ta Jamus dangane da yaki da ta'addanci da kokarin ganin an tabbatar da tsaro da zaman lafiya a duniya baki daya.

Bayanai na nuna cewa, mutane 12 ne suka mutu, kana kimanin 50 suka jikkata a harin na ranar Litinin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China