Shugaban kasar Sin ya mika sakon jajantawa ga takwaransa na Indonesia sakamakon abkuwar girgizar kasa a Aceh
A jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon jaje ga takwaransa na kasar Indonesia Joko Widodo, sakamakon abkuwar girgizar kasa mai tsanani a Aceh a ranar Laraba. A cikin sakon, shugaba Xi, ya bayyana cewa, ya girgiza matuka da jin labarin abkuwar bala'in a lardin Aceh, wanda ya haddasa mutuwa da jikkatar mutane masu yawa, baya ga hasarar dukiyoyi. A madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, da kuma shi kansa, shugaban na Sin ya mika ta'aziyar ga iyalan wadanda suka mutu, tare da fatar samun sauki ga wadanda suka samu raunuka.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Indonesia aminiyar kasar Sin ce. Sin za ta ba da taimako bisa bukatun kasar Indonesia. Ya yi imani cewa, jama'ar kasar Indonesia za su yi nasarar yaki da bala'in, tare da farfado da gidajensu.(Fatima)