Wata majiya daga rundunar sojan kasar ta Kamaru ta ce, an kai harin ne da misalin karfe 8 na safiyar agogon kasar, inda 'yan kunar bakin waken biyu suka tayar da boma bomai dake jikinsu a kofar shiga wata kasuwa dake garin Mora.
Sai dai baya ga mutuwar 'yan kunar bakin waken biyu, kawo yanzu ba'a samu rahoton mutuwa ko jikkatar ko da mutum guda ba.
Ana zargin wadannan 'yan kunar bakin waken biyu dakaru ne na kungiyar Boko Haram.
A watan Faburairun shekara ta 2015, a birnin Yaounde na jamhuriyar Kamaru, membobi na kwamitin kasashen dake gabar tafkin Chadi gami da kasar Benin, suka sanar da kafa rundunar hadin gwiwa mai kunshe da sojoji sama da 8700, da zummar murkushe kungiyar Boko Haram. A garin Mora ma an jibge sojojin kasashe daban-daban. (Murtala Zhang)