in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kunar bakin wake 2 sun mutu a Kamaru
2016-11-25 09:38:19 cri
Wata majiyar tsaro ta tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, mutane biyu sun mutu sannan wasu mutanen biyu sun samu raunuka a sanadiyyar hare haren kunar bakin wake sau biyu wanda aka kaddamar da safiyar jiya Alhamis a jamhuriyar Kamaru.

Harin ya faru ne da misalin karfe 7 na safe a garin Mora, wanda ke yankin arewa mai nisa a jamhuriyar Kamara mai makwabtaka da Najeriya, ana zargin wasu mata biyu 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar da harin.

An kashe daya daga daga cikin maharan ne, a dai dai lokacin da ta yi yunkurin kutsawa kasuwa garin Mora. Kana harin na biyu ya hallaka 'yar kunar bakin waken da kuma raunata fararen hula biyu.

Sai dai har yanzu ba'a sanar da harin ba a hukumance.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China