Jami'in hukumar ba da agajin gaggauwa ta Najeriya (NEMA) a yankin arewa maso gabashin kasar Sa'ad Bello, ya shaidawa manema labarai cewa, galibin mutanen da suka bar muhallan nasu mata ne da kananan yara, kuma yanzu haka an tsugunar da su a wasu sansanoni 4 da aka tanadar a jihar.
Jami'in hukumar ta NEMA ya ce, har yanzu ba a kai ga tantance yawan mutanen da suka jikkata sanadiyar fadan ba.
A farkon wannan makon ne dai fadan ya barke, lokacin da aka ba da rahoton cewa, makiyayan sun kaddamar da harin ramuyar gayya kan manoma da ke kauyen Dan-Anacha da ke gundumar Gassol a jihar Taraba. Ana dai zargin manoman ne da kashe wasu makiyaya da suka shiga gonakansu. (Ibrahim Yaya)