Wani dan sanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labaru cewa, an samu fashewar bom da aka dasa a wata mota a wurin ajiye motoci na wani shagon dake kan titin Palesdinu, daga baya kuma wani dan kunar bakin wake ya tayar da bom a cikin mota a titin dake kusa da shago din.
Wannan ganau ya kara da cewa, 'yan sanda sun riga sun killace wurin da aka tayar da bom din, kuma har zuwa yanzu babu kungiyar da ta sanar da daukar alhakin kai wadannan hare hare. (Bilkisu)