in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 5 sun mutu a sakamakon fashewar bom a yammacin kasar Iraki
2016-08-26 13:25:47 cri
A jiya Alhamis ne hukumar tsaron kasar Iraki ta bayyana cewa, wani bom da aka dasa a cikin mota ya fashe a birnin Fallujah dake jihar al-Anbar ta yammacin kasar Irakin, wanda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 5 yayin da mutane 8 suka samu raunuka.

Wani jami'in tsaro dake wurin ya bayyana cewa, maharin ya kutsa da motar ne har cikin tashar bincike ta soja dake birnin Fallujah, kafin ya tada bom din dake boye cikin motar, lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji 5, yayin da mutane 8 suka ji rauni. Kaza lika a wannan rana, sojojin kasar sun dakile wani harin bom na daban, wanda aka dasa cikin wata mota a yammacin birnin Fullujah.

A farkon wannan wata ne sojojin tsaron kasar Irakin suka kai hari kan dakarun kungiyar IS dake yankin arewa maso gabashin birnin Fallujah, kana dakarun dake boye a arewacin jihar al-Anbar sun yi musayar wuta kadan tare da sojojin gwamnatin kasar.

Birnin Fallujah dake jihar al-Anbar mai nisan kilomita 50 daga babban birnin kasar Bagadaza, ta fada hannun dakarun kungiyar IS a watan Janairun shekarar 2014. Daga bisani kuma sojojin gwamnatin kasar ta Iraki sun kwato birnin Ramadi, fadar mulkin jihar Al-Anbar a watan Disamba na shekarar 2015, kafin daga bisani su kwato birnin na Fallujah a ranar 17 ga watan Yunin bana. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China