in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu a harin birnin Baghdad ya karu zuwa 166
2016-07-05 10:04:14 cri
A jiya Litinin 4 ga wata, wani jami'in Iraki ya bayyana cewa, baki daya mutane 166 ne suka mutu sakamakon abkuwar harin boma-bomai da aka dasa cikin mota sau biyu a birnin Baghdad a safiyar ranar 3 ga wata, yayin da wasu 230 suka jikkata. Wannan ne harin ta'addanci mafi muni da aka kai a Iraki a bana.

Ofishin firaministan kasar Iraki ya shelanta zaman makoki na tsawon kwanaki uku daga ranar 4 ga wata a duk fadin kasar Iraki, tare da kara karfin daukar matakan tsaro a birnin Baghdad da yin bincike kan boma bomai.

Tuni dai kungiyar IS ta dauki alhakin kai wadannan hare hare.

Kawo yanzu kungiyar IS na da ikon babban yankin dake yamma da kuma arewacin Iraki, kuma tana ci gaba da yin gumurzu da sojojin kasar a wasu jihohi da yawa. A karshen watan Yuni, gwamnatin Iraki ta sanar da karbe birnin Fallujah daga hannun kungiyar IS bayan birnin ya kwashe tsawon shekaru biyu a karkashin IS. Amma duk da nasarorin da sojojin na Iraki suke samu, har yanzu kungiyar IS na ci gaba da mai da martani cikin tsanani ta hanyar kai hare hare.

Bisa alkaluman da tawagar taimakawa Iraki ta MDD ta bayar, an ce, rikice-rikice da hare-haren ta'addanci da aka yi a kasar Iraki a watan Yuni na bana sun haddasa mutuwar mutane 662, yayin da wasu 1457 suka jikkata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China