in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron Faransa: Gamayyar kasa da kasa za ta kai babban samame domin kwato Mosol
2016-10-01 13:02:43 cri
Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian a jiya Jumma'a ya bayyana wa manema labaru cewa, gamayyar kasa da kasa dake karkashin jagorancin Amurka, wadda ke da nufin murkushe kungiyar mai tsattsauran ra'ayi ta IS za ta dauki wani babban mataki a kasar Iraki a kwanaki masu zuwa, domin kwato muhimmin birnin Mosol, wanda a yanzu haka yake a hannun kungiyar IS.

A wannan rana wasu kafofin watsa labaru da dama na kasar Faransa sun bayyana cewa, za a kai babban yakin kwato Mosol a watan Oktoba. Haka kuma, a wannan rana da safe, jiragen saman yaki guda 8 na kasar Faransa sun tashi daga babban jirgin ruwan yaki mai saukar da jiragen sama yaki na Charles de Gaulle, wanda aka tura a gabashin Tekun Bahar Rum, domin gudanar da aiki. Game da haka, Le Drian ya bayyana cewa, an aike da wadannan jiragen saman yaki domin ba da hadin kai wajen yaki da ta'addanci ne, amma ba soma yakin karbo Mosol ba.

An ce, domin cimma burin kwato Mosol yadda ya kamata, rundunar sojojin kasar Amurka ta kara aike da masu aikin soja sama da 600 zuwa kasar Iraki, inda za su samar da taimako ga rundunar sojojin Iraki ta fannonin samar da bayyanai, ba da horo da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China