in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Libiya ya kai ziyara Algeriya
2016-12-26 09:25:02 cri
Firaministan kasar Libiya Fayez al-Saraj, ya sauka a birnin Algiers na kasar Aljeriya, domin ganawa da manyan jami'an kasar, a wani mataki na bunkasa yunkurin da ake yi na magance matsalolin tsaro, da wanzar da zaman lafiya a kasar ta Libiya.

Jim kadan bayan saukarsa a filin jirgin saman Houari Boumedien dake birnin na Algiers, Al-Seraj ya shaidawa 'yan jaridu cewa, ziyayar aikin da zai gudanar, ci gaba ce kan tattaunawar da sassan biyu ke yi domin ganin sun fidda Libiya daga rikicin siyasar dake addabar ta tsawon shekaru sama da 5.

Ya ce ya zama wajibi ya jinjinawa rawar da Aljeriya ke takawa, wajen tallafawa gwamnatin hadin kan kasa dake jagoranci a Libiya, yana mai fatan kara tattaunawa da mahukuntanta kan wasu hanyoyi na kawo karshen rikicin siyasar da Libiyan ke fama da shi.

Firaministan Aljeriya Abdelmalek Sellal, da kuma minista mai kula da yankin Maghreb da kungiyar AU a Aljeriyan Abdelkader Messahel ne suka tarbi Mr. Al-Seraj.

Wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fitar, ta bayyana wannan ziyara a matsayin wata dama da Aljeriyar za ta yi amfani da ita, wajen jaddada goyon bayanta ga manufar wanzar da zaman lafiya, da tabbatar da cikakken ikon mulkin kan kasar ta Libiya.

Libiya dai ta tsunduma cikin yakin basasa, tun bayan hambarar da tsohon shugaban ta Muammar Gaddafi daga karagar mulki a shekarar 2011 da ta gabata. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China