in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ruwa sun turo gawawwakin 'yan cin rani 16 a bakin tekun Libiya
2016-10-31 10:03:07 cri
Ruwa sun turo gawawwakin 'yan cin rani 16 a bakin tekun Libiya, dake kusa da birnin Zouara, dake yammacin kasar, a cewar kungiyar Red-Cross reshen Libiya.

Al-Khamis al-Bosaifi, kakakin Red Cross ta Libiya, ya bayyana cewa gawawwakin an gano su ne a ranar Asabar. Kuma ana kyautata zaton cewa 'yan ci ranin sun fito daga kasashen dake kudu da hamadar Sahara.

Mista Al-Bosaifi ya kara da cewa gawawwakin ma sun fara rubewa, kuma ba a da bayani kan dalilin nutsewar tasu.

A ranar Laraba, sojojin ruwan Libiya sun sanar da cewa 'yan ci rani 90 aka rasa labarinsu tun bayan jirgin ruwan dake dauke da su ya nutse. Wannan dake dauke da 'yan ci rani 129, ya nuste a gabar Garabulli, mai tazarar kilomita 50 daga gabashin Tripoli, babban birnin Libiya.

Kasar Libiya na daya daga cikin muhimman yankunan da 'yan ci rani suka fi so a cikin yunkurinsu na ratsa tekun Bahar Rum domin shiga Turai, suna gujewa tashin hankali da rashin tsaro da ake fama dasu a kasashensu na asali.

Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD (HCR) ta sanar da cewa 'yan cin rani 3740 sun mutu a shekarar 2016 a lokacin da suke kokarin ratsa tekun Bahar Rum. Adadin mutuwar na cigaba da karuwa a kan hanyar tekun Bahar Rum ta tsakiya, dake hada Libiya da Italiya, inda a matsakaici ake kirga mutuwar dan cin rani guda bisa 'yan cin rani 47 da suka isa, in ji HCR. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China