Mr. Lamamra ya shaidawa kafofin watsa labarai bayan ganawarsa da mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Thomas Shannon cewa, ya kamata a gudanar da matakan soja na yaki da ta'addanci a kasar Libya bisa tsarin dokar kasa da kasa, a sa'i daya kuma, a girmama 'yanci da kuma zaman karko na kasar Libya. Kaza lika, ya ce, kasashen Algeriya da Amurka suna goyon bayan ganin an warware matsalar Libya ta hanyar siyasa.
A nasa bangare kuma, mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Thomas Shannon ya ce, shi da Lamamra sun tattauna kan yadda za a warware matsalar Libya, yaki da ta'addanci da kuma taimaka wa kasar Libya wajen kafa gwamnatin hadaka da za ta kunshi dukkan al'ummomin kasar. (Maryam)