Wannan taro, bisa kiran kungiyar AU, zai hada kwamitin kasashe biyar wato Mauritaniya, Mali, Burkina Faso, Chadi da Nijar, da kuma kasashen dake makwabtaka da Libiya wadanda suka hada da Tunisiya, Aljeriya, Masar, Sudan, Chadi da Nijar, na cikin tsarin sanya ido kan ricikin Libiya, in ji babban jami'in Aljeriya din a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen Libiya, Mohamed Tahar Siyala dake rakiyar shugaban kwamitin mulki na gwamnatin hadaka na kasar Libiya, Faiz Serradj dake ziyarar aiki ta kwanaki biyu a yanzu haka a kasar Aljeriya.
Baya ga taron da aka tsaida shiryawa a Niamey, mista Messahel ya sanar da cewa shugabannin kwamitin kasashe biyar zasu gudanar a karshen watan Oktoba, da wani taron da ya shafi sanya ido kan matsalar Libiya, sai dai ba a ba da wani karin haske ba kan inda za a yi wannan taron.
A nasa bangare, shugaban diflomasiyyar Libiya ya nuna yabo kan rawar da Aljeriya take takawa game da kokarin warware rikicin Libiya. (Maman Ada)