in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a shirya taron kasa da kasa kan rikicin Libiya a Niamey a ranar Laraba mai zuwa
2016-10-19 09:34:44 cri
Babban birnin kasar Nijar, Yamai zai karbi a ranar Laraba mai zuwa da wani zaman taron kasashen dake makwabtaka karo na 9 kan rikicin Libiya. Wannan zaman taro da zai gudana a karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Nijar, Ibrahim Yabouba, zai sami halartar takwarorinsa na kasashen Aljeriya, Masar, Tunisiya, Libiya, Chadi da Sudan, da kuma wakilin musamman na sakatare janar na MDD game da Libiya, kana shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Libiya (MANUL), mista Martin Kobler, tsohon shugaban Tanzaniya, manzon musamman na kungiyar tarayyar Afrika (AU) game da kasar Libiya, Jakawa Kikwete da kuma sakaren janar a kungiyar kasashen Larabawa, Ahmed Abu El Gheit. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China