Ministar kudin kasar Femi Adeosun ce ta bayyana hakan ga taron manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar, bayan da taron majalisar zartarwar kasar wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ya amince da shirin.
Karkashin shirin gwamnati za ta baiwa duk wanda ya fallasa asirin barayin gwamnati ladan kaso biyar cikin 100 na kudaden da aka gano. Haka kuma gwamnati za ta dauki matakan da suka wajaba don an kare wadanda suka fassala barayin daga duk wani abu da ka iya samunsu. (Ibrahim)