Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya amince da nadin da aka yi wa Amina Mohammed, daya daga cikin ministocin kasar a matsayin sabuwar mataimakiyar babban sakataren MDD.
Shugaba BUhari ya bayyana a cikin wata sanarwar da aka raba wa manema labarai a yau Jumma'a cewa, Najeriya za ta ci gaba da hada kai da MDD, kana yana tabbacin cewa, Amina za ta daga martabar Najeriya a idon duniya.(Ibrahim)