in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wurin ibada da ya shahara a fannin wasan Kunfu
2016-12-23 14:11:07 cri

Tun da muna kiran Kunfu da sunan 'fasahar Kunfu", wannan ya nuna cewa Kunfu din wata fasaha ce, wadda ke da amfani ga zaman rayuwar dan Adam. Saboda Shaolin Temple yana da daruruwan sufaye wadanda suka kware a fannin fasahar Kunfu, hakan ya sa wurin ibadar taka muhimmiyar rawa a harkokin kasar Sin, musamman ma a fannin harkar siyasa.

Tun lokacin da kasar Sin ke karkashin masarautar Sui, wani dan sarki mai suna Li Shimin, ya taba gayyatar wasu sufaye 13 na Shaolin Temple, wadanda suka kasance kwararru ne a fannin wasan Kunfu, domin su halarci rundunarsa ta yakar sojojin wani sariki na daban. A fagen fada, sufayen 13 sun shaida kwarewarsu sosai, inda suka kutsa kai cikin sojojin abokan gaba gami da ceton dan sarkin, wanda aka kama aka tsare shi.

Daga bisani, dan sarkin ya hau karagar mulki, ya zama sarkin daular Tang. Don nuna godiya ga wadannan sufaye, sarkin ya samar da kudi da gonaki ga wurin ibada na Shaolin, da ba Shaolin Temple damar samun wata rundunar sufaye ta kanta.

Daya daga cikin rawar da sufayen Shaolin Temple suka taka akwai kokarin kare kasar Sin daga harin da wasu sojojin kasashen waje suka kai wa kasar. Ga misali, a lokacin daular Ming, wasu 'yan fashin teku 'yan kasar Japan, suna rika kai hare-hare ga wuraren dake bakin teku na kudu maso gabashin kasar Sin. Don tallafawa kokarin dakile 'yan fashin tekun, wasu sufayen Shaolin Temple 30 sun isa inda aka fi samun matsalar fashin. A cikin yake-yaken da suka yi da 'yan fashi, sun yi amfani da sandar karfe wajen kashe 'yan fashi da yawa. Kana a karshe, yayin wani yaki inda 'yan fashin suka fi su yawa sosai, sufayen sun yi ta fada har dukkansu suka mutu, inda suka sadaukar da rayukansu don tsaron kasa.

Zuwa yanzu za a iya ganin labarin wadannan sufaye cikin bayanan da aka saka kan wasu duwatsun da aka ajiye cikin wurin ibada na Shaolin.

Yanzu haka Shaolin Temple ya riga ya zama wata cibiyar koyar da fasahar Kunfu a kasar Sin. A cikin wurin ibadar, a kan bude darasi ga masu sha'awar koyon fasahar Kunfu na kasar Sin da na kasashen waje. Ban da haka kuma, a wuraren dake dab da Shaolin Temple, an kafa makarantu na masu koyar da fasahar Kunfu da yawa, wadanda suke samar da gudunmowa ga kokarin yada fasahar Kunfu na kasar Sin.(Bello Wang)


1 2 3 4 5 6
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China