in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wurin ibada da ya shahara a fannin wasan Kunfu
2016-12-23 14:11:07 cri

Ga duk wanda ya samu damar zuwa Shaolin Temple, zai ganewa idanun sa wasu kayayyakin tarihi masu yawa, wadanda suka zama shaidu kan yadda sufayen wurin suka yi kokarin koyon fasahar Kunfu a baya. Ga misali, akwai wani babban zane a kan wani bango, inda aka yi zanen wasu sufaye 30 da suke fada da juna, ko kuma a ce suna kokarin gwada fasahar Kunfu da juna. Ban da wannan kuma, akwai wasu zane-zanen da suka nuna yadda sufaye suke amfani da makamai daban daban, irinsu sanda, wuka, takobi da dai sauransu, a kokarinsu na koyon fasahar Kunfu.

Abin da ya fi ban mamaki shi ne, cikin wani babban daki na wurin ibada na Shaolin, za a iya ganin ramuka da yawa, wadanda suke kan wasu layi 2 a daben daki. Wannan daki, an ce shi ne wurin da sufaye suke gwada wasan Kunfu a lokacin baya. Kana yadda sufayen suke kokarin taka kasa yayin koyon fasahar Kunfu, ya sa aka samu ramuka kan daben dakin, duk da cewa daben nan an yi shi ne da duwatsu.


1 2 3 4 5 6
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China