in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wurin ibada da ya shahara a fannin wasan Kunfu
2016-12-23 14:11:07 cri

Sa'an nan tsakanin shekarar 546 zuwa ta 604, kasar Sin tana karkashin mulkin daular Sui, amma wata daula ta daban mai suna Tang tana daf da kama mulki a kasar, don haka yanayin kasar a lokaci na yawan fsukantar rikice-rikice.

Don kare wurin ibadar daga harin 'yan fashi, an zabi wasu sufaye masu karfin jiki da iya fasahar fada, domin su rika sintiri a sassan ginin. Da farko dai, wadannan sufaye suna kokarin tsaron wurin ibadar ne kawai, amma daga bisani bukatar da ake da ita a fannin siyasa ta sa aka rika tura su taimakawa wasu sarakuna wajen fada.

Bayan da sarakunan suka samu 'yancin mulki, sai suka baiwa wurin ibadar na Shaolin 'yancin samar da wata rundunar sufaye, wadanda suka iya fada da sanin fasahar amfani da makamai.

Daga bisani, sufayen Shaolin sun rika samun horo a fannin fasahar Kunfu, lamarin da ya zama wata al'adar wurin. Wasu daga cikinsu sun yi fice wajen fasahar Kunfu, har ma sun kai ga kirkiro wasu sabbin fasahohi a fannin Kunfu, wannan ya sa aka kara samun fasahohin wasannin Kunfu a wurin ibadar na Shaolin.


1 2 3 4 5 6
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China