in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wurin ibada da ya shahara a fannin wasan Kunfu
2016-12-23 14:11:07 cri

Kamar yadda muka ambata a baya, sufayen Shaolin Temple sun kwashe shekaru fiye da dubu daya suna kokarin nazarin fasahar Kunfu, saboda haka, sun kirkiro fasahohi daban daban. Cikinsu akwai fasahar da ta shafi yadda ake sarrafa numfashi, da fasahar kai hari da hannu ko kuma kafa, da fasahar tsalle-tsalle, da fasahar yin amfani da makamai irinsu sanda, wuka, takobi da dai sauransu. Baki daya fasahohin Kunfu na Shaolin sun kai fiye da dari.

Hakika kasancewar Shaolin Temple wani wurin ibada, amma sufayen wajen sun yi ta kokarin binciken fasahar fada, wannan wani abun mamaki ne. Sai dai wasan Kunfu na kasar Sin bai shafi fada kadai ba, cikin abubuwan da ya kunsa wadanda suka fi muhimmanci akwai gina jiki da kare kai. Bisa wannan manufa, za mu iya fahimtar dalilin da ya sa sufayen Shaolin suke kokarin koyon fasahar Kunfu.

A gaskiya idan da sufayen wurin ibada na Shaolin ba su taba nazarin fasahohin kunfu ba, da watakila a lokacin da kasar take cikin yanayi na yake-yake, tuni da an riga an wawashe Shaolin Temple ko ma a kone shi, ko a kakkashe sufayen wurin, ta yadda ko sunan wurin ibadar ba za a sake jin duriyar sa ba, balle ma fasahohin kunfu iri-iri.

Sai dai a nasu bangare, sufayen wurin ibadar Shaolin sun yi taka tsan-tsan wajen yada fasahohinsu ga sauran mutane, don magance yiwuwar shigar miyagun mutane har su kai ga iya fada. Bisa wannan dalili ne, sufayen suka tsara wasu ka'idoji kan yada fasahar Kunfu, inda suka kayyade cewa, kar a koyar da fasahar Kunfu ga mutane masu mummunar halayya, ko kuma wadanda ba sa kaunar iyayensu, da mutane marasa juriya, da wadanda ke da duhun kai, da wadanda ke kwadayin kudi, da wadanda ke da wayo da son cutar mutane, da mutane marasa mutunci. Duk wadannan mutane, an hana a koyar da su da fasahar Kunfu.


1 2 3 4 5 6
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China