Lamarin ya nuna yadda sufayen Shaolin Temple suke koyon fasahar Kunfu cikin matukar kokari. Haka kuma ya nuna cewa, zuriyoyin sufaye suna kokarin bin al'adar Shaolin Temple ta koyon fasahar Kunfu. Domin kamar yadda ake cewa 'bugu shi ke sa fata taushi', wadannan ramuka da ake samu a daben daki, ba nan take ake iya samun su ba. Ana samun su ne bayan shekara da shekaru sufayen suna ta kokarin gwada fasaharsu a cikin daki.
Cikin shekaru fiye da duba 1 da suka wuce, a wasu lokuta, an rika samar da dama ta raya wurin ibada na Shaolin don ya samu karin sufaye, da damar kyautata gine-ginensa. Sai dai zuwa wani lokaci, saboda yake yake da suka auku, ko kuma sauyin ra'ayi na masu mulki dangane da addinin Budda, wurin ibadar na Shaolin ya rika lalacewa, kana sufayen sun rika tarwatsewa.
Sai dai duk irin wannan yanayi, sufayen Shaolin Temple sun yi kokarin kiyaye fasahohinsu a fannin Kunfu, tare da yada su zuwa wurare daban daban na kasar Sin. Dalilin hakan ya sa ake cewa "kusan dukkan fasahohin Kunfu na kasar Sin na da asalin su daga Shaolin Temple."