in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU ta bada tallafin dala 200,000 ga shirin WFP
2016-10-21 11:10:39 cri
Kungiyar hadin kan tarayyar Afirka ta AU, ta bada tallafin dalar Amurka 200,000 ga shirin abinci na duniya WFP, domin agazawa 'yan gudun hijirar dake yankunan tafkin Chadi.

Jakadan kasar Ghana a kungiyar AU Albert Yankey, ya ce tallafin kudin zai karfafa ayyukan WFP wajen yaki da karancin abinci mai gina jiki, da samar da abinci ga 'yan makaranta a wuraren 'yan gudun hijira.

Mr. Yankey, wanda ya nazarci halin da ake ciki game da bukatun 'yan gudun hijira a Bagassola dake yankin na tafkin Chadi, ya ce ya yi imani da tasirin ayyukan bada agaji da WFP, tare da sauran hukumomin MDD ke bayarwa ga 'yan gudun hijira.

Al'ummun wannan yanki mai iyaka da kasashen Chadi, da Nijar, da Najeriya, da Kamaru, na fusknatar tashe tashen hankula daga mayakan Boko Haram. A kuma watan Janairun bara ne WFP ya kaddamar da shirin raba abinci mai gina jiki ga mutane da yawan su ya kai 130,000, adadin da ya kunshi 'yan janhuriyar Nijar su 6,500.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China