Jiya Lahadi shugaban hukumar kula da asusun tabbatar da tsaron zamantakewar al'ummar kasar Sin Lou Jiwei ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya suna kokarin kyautata tsarin tattalin arzikinsu, a saboda haka gwamnatin kasar Sin ita ma ta dauki matakai a jere, kuma ta samu sakamako mai faranta ran mutane.
Lou Jiwei ya fadi haka ne a yayin taron shekara shekara kan tattalin arzikin kasar Sin da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da kuma sabon taron jirgin ruwan "Bashan" na shekarar 2016 da aka gudana jiya a nan birnin Beijing.
Ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, bayan da ta dauki matakai a fannonin saukaka ayyukan hukumomin gwamnati, da sauko da ma'aunin kafa kamfanoni, da kara bude kasuwa, da kara sa kaimi kan gyare-gyaren fasahar kayayyaki, da kara cudanya tsakanin garuruwa da kauyuka, tare kuma da kara yin kwaskwarima kan tsarin yin rajistar iyali, da tsarin harkokin kudi, da kasafin kudi a kasar ta Sin.(Jamila)