in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan takakar zaben shugaban kasar Ghana sun yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya
2016-12-02 10:51:32 cri
'Yan takarar zaben shugaban kasar Ghana guda bakwai dukkansu sun yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya kafin lokaci da kuma bayan zabukan da aka tsaida a ranar Laraba mai zuwa.

Wannan yarjejeniyar zaman lafiya, a karkashin jagorancin kwamitin zaman lafiya na kasa, na da burin tabbatar da cewa dukkan jam'iyyun siyasa, shugabanninsu da kuma magoya bayansu za su amince da sakamakon zabe.

Na yi alkawari da babbar niyyata ga zaman lafiya, in ji shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama a gaban wata tawagar kasa da kasa ta manyan jami'ai dake kunshe da MDD, ECOWAS da kungiyar Commonwealth.

Mista Mahama, na neman sake zarcewa a karkashin inuwar jam'iyyar NDC, ya jaddada cewa a matsayinsa na shugaban kasa, zai rasa kome idan kasarsa ta fada cikin tashe tashen hankali.

Babu wani mulkin siyasa dake bukatar da a zubar da jinin 'yan kasar Ghana, in ji shugaba.

Tare da bayyana niyyarsa wajen tabbatar da zaman lafiya, sabon shugaban jam'iyyar adawa ta NPP, Nana Akufo-Addo, ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki niyyar tabbatar da zaman lafiya ba kawai ta baki ba.

Gwamnatin Ghana, hukumar zabe da 'yan sanda, sun kasance na sahun gaba, da nauyin tabbatar da zabuka cikin 'yanci da aldalci ya rataya kan wuyansu, in ji Nana Akufo-Addo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China