Kamfanin dillancin labarun Siriya ya ruwaito cikin sanarwar da sojojin Siriya suka fitar cewa, a wannan rana, kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi sun kai farmaki ga sojojin Siriya. An jefa igwa a unguwannin jama'a da wani asibitin dake birnin Halep. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka samu, an ce, harin igwar ya haddasa mutuwar mutane a kalla 20, tare da jikkatar wasu 40, akasarinsu mata ne da yara.
A wannan rana, bayan da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi shawarwari da manzon musamman na sakatare janar na M.D.D. game da batun Siriya Staffan de Mistura, ya fadawa manema labaru cewa, ba za a kawar da yiwuwar shirya taron kasa da kasa kan nuna goyon baya ga kasar Siriya ba, don tattauna matakan da za a dauka wajen ingiza farfado da shawarwari. Lavrov ya ce, ya zama dole a gudanar da kudurorin da aka cimma a yayin taron, ciki har da ka'idar da ake bi domin alummar Siriyar su warware rikicin da ya addabi kasarsu. (Bako)