A cikin sanarwar, kakakin majalisar gudanarwar Amurka Mark Toner ya bayyana cewa, Amurka tana fatan Rasha a matsayinta na shugabar rukunin kula da batun tsagaita bude wuta game da batun Siriya na kasa da kasa za ta ci gaba da matsa lamba ga gwamnatin Siriya ta martaba yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma, yayin da Amurka za ta bukaci bangaren 'yan adawa na kasar da su ma su yi hakan.
A jiya ne, sojojin Siriya suka sanar da cewa, tun daga karfe 1 na safiyar yau Alhamis, za su tsagaita bude wuta har na tsawon sa'oi 48 a yankin Allepo da ke yankin arewacin kasar.(Bako)