A yau Laraba ne ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai gabatarwa majalisun dokokin kasar biyu shirin kasafin kudin kasar na shekarar 2017.
Wannan shi ne karo na biyu da shugaban ke gabatarwa majalisun kasafin kudi tun bayan rantsar da shi a watan Mayun shekarar 2015.(The Punch)
A jiya ne gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi amfani da kudaden da aka kwato da kuma wadanda aka sabunta lasisin mai a kasafin kudin kasar na shekarar 2017 kudi,ko da ta kai ga cimma kudaden shigar da ta yi fatan samu a shekara mai zuwa.(Vanguard)
Mahukuntan Najeriya suna fatan daidaita kudin Intanet a kasar zuwa kashi 50 cikin 100 nan da shekarar 2020, ta hanyar amfani da makin da kasar ta samu a halin yanzu a harkar musayar intanet .
Ana amfani da bunkasuwar harajin intanet na kasa a matsayin mizanin auna karfin intent din kasa da kuma ci gaban tattalin arzikinta na zamani.(The Guardian)