in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya(20161215)
2016-12-15 19:02:05 cri

A jiya Laraba ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar wa majalisun dokokin kasar shirin kasafin kudin kasar na shekarar 2017 na tsabar kudi Naira triliyan 7.298 kwatankwancin dala biliyan 23, inda ake fatan samun kudaden daga bangaren da bai shafi mai ba.

Shugaban ya ce, an tsara kasafin kudin ne kan farashin dala 42.5 kan ko wace gangar danyen mai da kuma ganga miliyan 2.2 da kasar ke fatan hakowa a kowa ce rana wanda ake hasashen musayarsa kan matsakaicin farashin naira 305 kan ko wace dalar Amurka.(Daily Trust)

A jiya ne fadar shugaban Najeriya ta gayyaci manyan jami'an ma'aikatar wasannin kasar da hukumar kwallon kafan kasar, sakamakon zanga-zangar da 'yan wasan Super Falcons suka yi a harabar majalisar dokokin kasar, bayan da hukumar kwallon kafan kasar ta ki biyansu hakkokinsu bayan kammala gasar cin kofin kwallon kafar mata na Afirka da ya gudana a kasar Kamaru, inda 'yan wasan na Super Falons suka doke 'yan wasan kasar Kamaru da ci da nema.(The Guardian) (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China