in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeriya, da Najeriya zasu hada gwiwa don yakar ta'addanci
2016-12-14 10:35:17 cri
A jiya Talata shugaban kasar Algeriya Abdelaziz Bouteflika, ya gana da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, wanda ke ziyarar aiki a kasar, inda suka tattauna game da yadda za'a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, ciki har da batun hada kai don yakar ayyukan ta'addanci.

Osinbajo ya shedawa 'yan jaridu cewa, ganarwa tasu da shugaba Bouteflika wata dama ce da kasashen biyu zasu tattauna game da batun siyasa da kuma hadin gwiwa wajen yakar ayyukan ta'addaci tsakanin kasashen na Algeriya da Najeriya.

Ya ce "shugaba Bouteflika ya bayyana goyon bayansa ga Najeriya a kokarin da take yi na yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayin addini".

Najeriyar wacce ta shafe shekaru tana fama da hare haren ta'addanci, wanda kungiyar Boko Haram ke kaddamarwa kan fararen hula da gwamnatocin kasar.

Hari na baya bayan nan da aka kaddamar shi ne na ranar Juma'a, wanda ya hallaka fararen hula 45 a wani harin kunar bakin wake a jahar Adamawa dake shiyyar arewa maso gabashin kasar yayin da wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake suka tada boma boma a wata kasuwa dake garin Madagali.

Kasar Algeria ta yi Allah wadai da harin, kana ta bukaci kasashen duniya su kara daukar matakan yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayin addini.

Osinbajo ya ce kasashen Algeria da kuma Nigeria, suna da dangantaka mai dadadden tarihi, kuma akwai yarjejeniyoyi masu yawa da kasashen biyu suka kulla.

Shi dai mataimakin shugaban na Najeriya ya isa birnin Algiers a jiya Talata ne, don ziyarar aiki ta kwanaki biyu, bisa goron gayyatar da shugaban kasar Algeriyan Bouteflika ya aikawa Najeriyar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China