in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya(20161213)
2016-12-13 20:15:44 cri

Da alamun Najeriya ta fara ganin haske dangane da farfadowar tattalin arzikinta, yayin da farashin danyen mai ya yi tashin da ba a taba ganin irin sa ba cikin watanni 18,in a ya kai dala 58 kan kowa ce ganga, bayan da mahukuntan kasar suka tsara kasafin kudin kasar na shekarar 2017 kan dala 45 kan kowace gangar danyen mai da kuma hasashen kasar na hako ganga miliyan 2.2 a kowa ce rana.(Vanguard)

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Tukur Buratai ya bayyana cewa, dakarun kasar da ke yaki da mayakan Boko haram a yakin arewa maso gabshin kasar, za su koma baraki a shekarar 2017, lokacin da ake fatan za a kawo karshen yakin baki da daya.

A ranar Jumma'a ne dai wasu tagwayen bama-bamai da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka dana, suka halaka mutane 54 tare da jikata 77 a kasuwar Madagali da ke jihar Adamawa. Babban hafsan ya ce, dakarun suna da tabbacoin samun nasara a kan 'yan ta'addan.(The Punch)

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, ta bayyana a jiya Litinin cewa, ba ta da wani shiri na hukunta wasu 'yan wasan 'yan wasan Suoper Falcons da masu horas da su kan rawar da suka game da rashin biyan su hakkokinsu.(The Guardian)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China