Mai magana da yawun shugaban babban taron MDD Dan Thomas, ya sanar da cewa sabon sakatare janar na MDD Antonio Guterres zai sha rantsuwar kama aiki a ranar Litinin mai zuwa, wato 12 ga wannan watan na Disamba a lokacin taro na musamman na MDD.
Taron zai karrama magatakardan MDD mai barin gado Ban Ki-moon, sannan nan za'a rantsar da sabon babban sakataren Guterres.
Thomas ya ce, an shirya gudanar da taron ne da misalin karfe 10 na safe, kuma za'a gudanar da taron ne a helkwatar MDD dake birnin New York.
A ranar 13 ga watan Oktoba ne babban taron MDD ya amince da zabar mista Antonio Guterres, wanda kuma tsohon firaiminsitan kasar Potugal ne, inda zai kasance a matsayin sakatare janar na MDD na 9, zai maye gurbin mista Ban wanda ya kare wa'adin aikinsa a karshen wannan shekara.
Guterres zai jagoranci MDD na tsawon shekaru 5, kana wa'adin aikinsa zai fara ne daga ranar 1 ga watan Janairun badi zuwa 31 ga watan Dismabar shekarar 2021.(Ahmad Fagam)