in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana zata yi zabe na musamman a ranar 1 ga watan Disamba
2016-11-25 10:18:31 cri
Hukumar zaben kasar Ghana (EC), ta ce zata gudanar da zabe na musamman a ranar 1 ga watan Disamba, kwanaki 6 gabanin gudanar da babban zaben kasar.

Mataimakin daraktan yada labarai na hukumar ta EC Yussif Ayuba, shi ne ya tabbatar da hakan ta cikin wani shirin gidan radiyon tarayya na kasar a jiya Alhamis, ya ce tuni aka tura kayayyakin aikin gudanar da zaben zuwa yankunan da aka kebe don yin zaben a duk fadin kasar.

Ya kara da cewa, hukumar zaben kasar tana yin aiki kafada da kafada da hukumar 'yan sandan kasar domin samar da ingantaccen tsaro a lokacin zaben.

Ayuba, ya baiwa al'ummar kasar Ghana da kasashen duniya tabbatacin hukumar na gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe a kasar.

Zaben na musamman zai baiwa jami'an tsaron kasar, da 'yan jaridu, da kuma ma'aikatan da zasu gudanar da aikin zaben kasar damar kada kuri'unsu ne, gabanin ranar babban zaben kasar.

EC, ta ce kimanin jami'ai 65,000 ne zasu kada kuri'unsu a lokacin zaben na musamman na wanann shekara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China