in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Erdowan ya yi Allah wadai da kisan jakadan Rasha da ke Turkiya
2016-12-20 09:21:02 cri
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiya ya yi Allah wadai da kakkausar murya game da kisan da aka yi wa jakadan kasar Rasha Andrey Karlo da ke Turkiya.

Shugaba Erdogan ya bayyana kisan jakadan a matsayin takalar fada da nufin lalata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Erdogan ya ce, ya tattauna da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda ya ba da umarnin tura jami'an tsaron kasar Turkiya don su gudanar da bincike game da lamarin.

Rahotanni na cewa, wani dan bindiga ne sanye da bakar kwat da laktaya ya harbe jakadan kasar ta Rasha da ke Turkiya lokacin da ya ke jawabi a bikin bude kolin zane-zane a birnin Ankara.

Kafofin tsaron Turkiya sun bayyana cewa, dan bindigar yana kabbara da kururuwar cewa, kar ku manta da Aleppo da Syria da 'yan uwanmu, kana daga bisi ya bude wuta.

Ministan harkokin cikin gidan na kasar Turkiya Suleyman Soylu, ya bayyana cewa, an harbe dan bindigar mai shekaru 22 da haihuwa har lahari a wurin da lamarin da faru. An kuma gano cewa, dan bindigar jami'in dan sandan Turkiya ne mai Mevlut Mert Altintas. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China