in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta yi suka kan harin sama da sojojin Amurka suka kai ga sansanin sojojin gwamnatin Syria
2016-09-19 09:01:46 cri

A jiya Lahadi ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar da wata sanarwa, inda ta bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, dakarun 'yan adawan kasar Syria ba su tsagaita bude wuta ba kamar yadda yarjejeniyar da aka daddale ta tanada a daidai wannan lokaci.

Kaza lika sojojin kawancen kasa da kasa da aka kafa musamman domin dakile IS dake karkashin jagorancin kasar Amurka, sun kai hari ta sama ga sansanin sojojin gwamnatin Syria, hakan ya sa yanayin da Syria ke ciki ya kara tsanani, wanda hakan ya sa yarjejeniyar da Rasha da Amurka suka daddale kan batun Syria ta gamu da matsala.

Sanarwar ta yi kashedin cewa, wajibi ne Amurka ta matsa lamba ga dakarun 'yan adawar Syria wadanda ke karkashin goyon bayanta, ta yadda za ta aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba tare da gindaya sharadi ba, in ba haka ba, yarjejeniyar da aka cimma kan batun Syria ba za ta yi tasiri ba ko kadan.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China