in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta zargi Amurka da kawo jinkiri ga warware rikicin Syria
2016-06-17 10:26:12 cri

Ministan harkokin wajen Rasha Serguei Lavrov ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Amurka ce da magoyanta, ba wai Rasha ba, suka kasance masu laifi kan jinkirin da aka samu wajen warware rikicin Syria cikin ruwan sanyi.

Jami'in diplomasiyyar Rasha, dake halartar dandalin tattalin arzikin kasa da kasa na St-Petersburg, ya yi wannan kalami domin yin watsi da sanarwar baya bayan nan ta sakataren kasar Amurka John Kerry ya yi na cewa, Amurka ta kusan gajiya da hakuri da Rasha da Bachar al-Assad, dake kasancewa kalubale ga kawo karshen yaki a Syria.

Ya kara da cewa, matsayin da Amurka da masu goyon baynta suka dauka shi ne nuna kasawarsu, ko kuma ba su iya yin matsin lamba ga abokansu na shiyyar, lamarin da ya kasance abu mai wuya na tattara dukkan bangarorin da rikicin Syria ya shafa kan teburin shawarwari.

Mista Lavrov ya bayyana cewa, a cikin watan Febrairu, mista Kerry da kansa ya jaddada wajabcin dukkan kungiyoyin da suka dunkule a bangaren ta'addanci tare da kungiyar Al-Nusra da kungiyar IS da su nisance su da kuma barin wadannan yankuna. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China