in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa jakadan Rasha dake Turkiya
2016-12-20 09:18:49 cri

A daren jiya Litinin ne, shugaban kasar Rasha Putin ya yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da kisan da aka yi wa jakadan kasarsa dake kasar Turkiya. Shugaba Putin ya jaddada cewa, zai kara daukar matakan yaki da ta'addanci domin hana sake aukuwar wannan lamari.

A wannan rana, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharowa ta bayyana cewa, kisan jakadan Rasha dake Turkiya tamkar harin ta'addanci ne, kuma Rasha za ta gabatar da batun ga kwamitin sulhun MDD domin ya gudanar da bincike.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China