Huang Shuxian ya bayyana cewa, kamata ya yi kasa da kasa su zurfafa da tabbatar da amincewa da juna a siyasance, da cika alkawarinsu a fannin siyasa, domin yaki da masu cin hanci da rashawa da suka tsere zuwa ketare, ta yadda ba za su iya tsira daga laifinsu ba. Ban da haka, kamata ya yi kasa da kasa su ci gaba da dora muhimmanci kan cafke masu aikata laifin da suka tsere zuwa ketare da maido da kudaden da suka gudu da su, ta hanyar amfani da yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya, kuma bisa tsarin hadin gwiwar kungiyar 'yan sandan duniya, da bankin duniya da sauransu, tare da kyautata tsarin gudanar da dokokin shari'a a shiyya shiyya da ma duniya baki daya a karkashin kungiyar APEC, da ta G20 da sauransu.
Wakilai daga kasa da kasa suna ganin cewa, cin hanci da rashawa, ainihin abu ne da ke haifar da yawan matsalolin da ake fuskanta a duniya. Kamata ya yi gwamnatocin kasashen duniya su gudanar da yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa ta MDD, da kara sa haske a ciki, da kara karfin yin hadin gwiwa a wannan fanni, da zummar kawar da wannan matsala yadda ya kamata.(Fatima)