in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta bukaci da a warware batun tekun kuduncin Sin ta hanyar shawarwari
2016-05-27 13:07:31 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta yi na'am da matsayar kasar Sin game da kudurin ta na ganin an warware batun tekun kudanci ta hanyar gudanar da shawarwari.

Ma'aikatar ta kara da cewa, matsayar rasha ta yi daidai da ra'ayin taron kungiyar hadin kai ta Shanghai ko (SCO), kamar yadda hakan ke kunshe cikin sanarwar bayan taron kungiyar ta SCO, wanda ministocin wajen kasashen kungiyar suka fitar, bayan taron su na ranar Talata a birnin Tashkent na kasar Uzbekistan.

Game da hakan, shi ma sakatare janar na kungiyar ta SCO Rashid Olimov, ya fidda wata sanarwa wadda take tabbatar da matsayin kasar ta Rasha.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China