in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Benin zai kaddamar da shirin raya kasa na biliyoyin dala
2016-12-19 10:08:35 cri
Shugaba Patrice Talon na kasar Benin ya bayyana kudurinsa na kaddamar da shirin raya kasa na shekaru biyar wanda zai lashe zunzurutun kudi har Sefa biliyan 9,039, kimanin dala biliyan 14.4. A wani mataki na bunkasa kasar da ke yammacin kasar da ke shekarar 2016 zuwa ta 2021.

A jawabinsa yayin kaddamar da shirin ministan kudi da tattalin arziki na kasar Romuald Wadagi ya bayyana cewa, yanzu haka gwamnati ta tanadi Sefa biliyan 889 kimanin dala biliyan 1.416, yayin ake sa ran ragowar Sefa biliyan 8,150, kwatankwacin dala biliyan 12.985 za su fito ne daga bangaren sassan masu zaman kansu da sauran abokan hulda.

Manufar shirin dai ita ce samarwa 'yan kasar musamman matasa masu hazaka yanayin da ya dace a kokarin da ake yi na sake kaddamar da shirin raya kasa mai dorewa.

A ranar Jumma'a ne dai aka kaddamar da shirin a birnin Cotonou mai taken fito da kasar Benin, bikin da ya samu halartar sama da wakilan hukumomin kasar 800, kungiyoyin fararen hula, ma'aikatan diflomasiya da ke aikin a kasar da kuma masu sha'awar zuba jari na gida da na waje da ke cikin kasar.

Kimanin manyan ayyukan 45 za a gudanar a karkashin wannan shirin, wadanda ake sa ran za su lashe tsabar kudi dala biliyan 11.29. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China