in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin na fatan kyautata tsaro a cikin filayen jiragen samanta
2016-11-20 12:34:07 cri

Gwamnatin kasar Benin ta dauki niyyar kyautata sha'annin tsaro a cikin filayen jiragen saman kasar, ta hanyar zamanintar da tsarin sanya ido kan yankunan iyakoki na filayen jiragen sama, in ji ministan kasa, kana sakatare janar a fadar shugaban kasa, Pascal Koupaki a ranar Jumma'a da yamma.

Gaban matsalolin yin rijista, karfafa tsaron ayyukan bincike da sanya ido na shige da ficen masu tafiye tafiye a cikin filayen jiragen sama, ya kasance wajibi. Aiwatar da wani tsarin sanya ido na shige da fice zai taimaka kuma wajen zamanintar da hanyoyin aiki da kyautata inganci da sanya ido yadda ya kamata, in ji ministan a yayin wani taron manema labarai bayan wani taron mambobin gwamnati na mako mako.

Game da wannan, mista Koupaki ya jaddada cewa gwamnatin Benin ta dauki matakin mika aikin ga wani kamfani da ya gabatar da wata hanyar fasahar tantance fuskokin jama'a, da samar da kayayyaki da kudi, da kafa tsarin da gwamnati da wasu ma'aikatun da abin da ya shafa za su amfani da shi, musammun ma wadanda nauyin tsaron dukiyoyi da mutane ya rataya kan wuyansu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China