Domin cimma wannan buri, gwamnatin Benin za ta aiwatar da wata sabuwar manufar tattalin arziki ta shekaru biyar, da zata shiga cikin tsarin shata manufofin tsara ayyuka na gwamnati, wanda babban burinsa shi ne na sake ingiza cikin karko cigaban tattalin arziki da na jama'ar Benin.
Musammun ma game da shekarar 2017, manufar tattalin arziki zata shafi, fannoni da suka hada da zuba jari kan noma da bunkasa bangarori hudu musammun ma noman masara, shimkafa, ayaba da kade, bunkasa masana'antun sarrafawa da zamanintar da ayyukan hannu, bunkasa abubuwa more rayuwar jama'a kamar hanyoyi, makamashi, musamman kimiyya da fasaha, bunkasa yawon shakatawa da dai sauransu. (Maman Ada)