in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alkalan Benin sun dakatar da yajin aikinsu na kwanaki uku tare da bada wani wa'adi ga gwamnati
2016-11-28 11:02:52 cri
Kungiyar alkalan kasar Benin (UNAMAB) ta dakatar da yajin aikinta na kwanaki uku da ta fara tun ranar 22 ga watan Nuwamban da ya gabata tare da ba da wani wa'adin wata guda da gwamnatin Benin, in ji wata sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi a Cotonou.

A cikin takardar yajin aikin da ta mikawa mambobin gwamnati, UNAMAB ta bukaci biyan albashi da kuma tikitan samun man fetur ga alkalan kasar, da biyan albashin watannin Janairu da Febrairun shekarar 2016 da kuma kasafin samarwa domin shekarar 2017, da soke da biyan kudin rijista da daga karshe kuma da biyan kudin rangwame na shekarar 2014 zuwa 2016 da kuma na shekarar 2004 zuwa 2011.

Game da haka, a cewar takardar dakatar da yajin aikin da aka fitar a ranar Lahadi a Cotonou, UNAMAB ta tunatar da gwamnatin Benin da ta amsa bukatunta yadda ya kamata musammun ma game da samun man fetur, koda yake ba a sanya shi ba cikin kasafin kudin kasa ba. An riga an fitar da kudin rijista kuma ana kan hanyar rarrabasu kana abin da ya rage shi ne sanya samar da man fetur a cikin kasafin kudin kasa na shekarar 2017. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China