in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga 'yan Afrika da su hana duk wani gyaran fuska domin tsaya kan mulki ga kundin tsarin mulkinsu
2016-11-30 11:17:51 cri

Shugaban kotun tsarin mulkin kasar Benin, Theodore Holo, ya yi kira a ranar Talata a birnin Cotonou, hedkwatar tattalin arikin kasar Benin, ga al'ummomin Afrika da su nuna adawa ga duk wani gyaran fuska domin tsayawa kan mulki ga kundin tsarin mulkinsu.

Mista Holo ya bayyana cewa, illar da ke bayyana a gaba da kuma ya kamata a yi rigakafi, su ne gyaran fuska ga dokokin tsarin mulkin kasa da wata manufa wanda burin shi ne batar da dokokin da ake son yi wa gyaran fuska, domin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki na shafar aiwatar abin da ya kamata a yi da abin da bai kamata a yi ba, don haka ya kamata a tsaya cikin ko ta kwana a ko da yaushe.

Da yake magana a yayin bude taron kara wa juna sani na manyan jami'ai na shiyya shiyya mai taken "gyare-gyaren kundin tsarin mulki: gaskiya da abin da ake son cimma", wannan shugaban babbar hukumar shari'a kan dokokin tsarin mulki na kasar Benin na goyon bayan tunanin cewa kundin tsarin mulki ba rumfunan yin barci ba ne.

Mista Holo ya kara da cewa, ba zai amince ko kadan ba da ra'ayin cewa kundin tsarin mulki, wato muhimmiyar yarjejeniya tsakanin gwamnati da al'umma, ta kasance a tsaye, da kuma ake canzawa. A maimako, ya kamata ta dace da sabbin bukatun al'ummomi da kuma tsayawa kan ginshikin tsarin demokaradiyya da kasa mai 'yanci. Haka kuma ta tabbatar da 'yancin fadin albarkacin baki da tushen hakkokin 'yan Adam. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China